Hukumar kwastam ta damke kwantena jigbe tufafin Sojoji a jihar Abia (Hotuna)
Kakakin hukumar kwastam na Najeriya, Mr Joseph Attah, ya bayyana cewa hukumar ta damke kwantena daya jibge da kayan Sojoji da wasu kayayyaki a ranan Juma’a, 27 ga watan Yuli, 2018 a Aba zuwa Fatakwal.
Attah, ya bayyana hakan ne a wata jawabi da ya saki a Abuja ranan Juma’a.
Yace: “Jami’an hukumar na Zone C sun damke kwantena mai lamba MRSU 3040288 dauke da tufafin Sojoji da wasu kayayyaki a hanyar Aba-Portharcourt.
“An tafi da kwantenan gari Owerri, inda aka gudanar da bincike gaban mai ita kuma ka ga dilolin sabbin kayan soji 11.”
“Kowani dila na kunshe sa tufafi 400 dinkakku, kwalayen takalman soji 15, katakon dakin girki 7, sabbin Tiles 337, kayayyakin asibiti 27 kirar China, tiyon ruwa 34 da wasu wasu kayayyakin amfanin gida.”
KU KARANTA: Allah ya yiwa shahrarren dan kwallo, Ahmed Musa, karuwa
Game da cewarsa, kwantrolan Zone C, Ahmed Azarema ya ce an garkame wanda aka kama da kayan kuma an kaddamar da bincike kan masu alaka da kayan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng