Gwamnan jihar Kwara: Mun gaji da APC, Saraki kawai muke jira ya fada mana alkiblar da zamu fuskanta

Gwamnan jihar Kwara: Mun gaji da APC, Saraki kawai muke jira ya fada mana alkiblar da zamu fuskanta

Rikicin da ke cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na cigaba da tafarfasa yayinda gwamnan jihar Kwara, AbdulFatah Ahmed, ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar a jihar sun gaji da jam’iyyar kuma saboda haka, za su iya barin jam’iyyar a koda yaushe.

Gwamnan wanda yayi jawabi a taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar a Ilori, babban birnin jihar yace sun fidda rai daga wani sulhu gabanin zaben 2019.

Yace: “Abin da baci rai kuma da takaici bamu cimma babban makasudin komawanmu APC daga PDP a 2014 ba.”

“Muna son dukkansu ku bada gudunmuwa saboda muyi ittifakin kan jam’iyyar da zamu koma ba tare da hayamiya ba.”

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun samu nasarar fitittkansu – Hukumar yan sanda

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa wasu gwamnonin jam’iyyar APC 3 sun gana da jigogin jam’iyyar PDP a jihar Kwara. Wannan ganawar da sukayi yasa an yi has ashen cewa suna shirin sauya sheka tsohuwar jam’iyyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba, gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP kuma zuwa ranan Lahadi, ana sa ran gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, sai sauya sheka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel