Da dumin sa: Mataimakin Gwamnan Kaduna ya bayyana kudurin tsayawa takara a 2019

Da dumin sa: Mataimakin Gwamnan Kaduna ya bayyana kudurin tsayawa takara a 2019

Mataimakin gwamnan jihar kaduna dake a Arewacin Najeriya, Barnabas Bantex a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana kudurin sa na tsayawa takarar kujerar Sanatan jihar ta shiyyar kudancin ta a zaben 2019 mai zuwa.

Barnabas Bantex ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin na Kaduna inda ya bayyana cewa yanzu ya cimma daidaito tsakanin sa da gwamnan jihar game da kudurin nasa.

Da dumin sa: Mataimakin Gwamnan Kaduna ya bayyana kudurin tsayawa takara a 2019
Da dumin sa: Mataimakin Gwamnan Kaduna ya bayyana kudurin tsayawa takara a 2019

KU KARANTA: EFCC ta biyo ta kan surukin Obasanjo

Legit.ng ta samu cewa sai dai Barnabas Bantex din yace yanzu ba zai yi murabus daga mukamin sa na mataimakin gwamna ba sai nan gaba kadan.

A wani labarin kuma, Jami'an hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Najeriya ranar Alhamis sun gurfanar da wani mutum mai suna John Abebe dake zaman suruki ga tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a kotu.

Mista John Abebe wanda kani ne ga marigayiya tsohuwar matar Cif Obasanjo, Stella Obasanjo din EFCC ta ce ta gurfanar da shi ne a kotun bisa zargin sa da suke yi da anfani da takardun bogi wajen neman aikin hakar mai daga Najeriya din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng