Ya zama dole kada majalisar dokoki ta tsige Buhari – Ohaneze
Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, babin jihar Anambra, Cif Damian Okeke ya gargadi majalisar dokokin kasar akan duk wani yunkuri na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Okeke yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Awka, ya ba da shawarar cewa hanyar mafi cancanta da ya kamata a bi wajen cire shugaban kasar, shine ta hanyar zabe.
Ya ci gaba da cewa duk wani makirci don tsige Buhari zai iya haddasa rikicin siyasa a kasar wadda yana iya zuwa ga juyin mulki.
A cewarsa, “Idan aka bi ta hanyar tsigewa, mutane za su maida martani Kaman mayuwatan zakuna sannan kuma za’a rasa ran bayin Allah.
KU KARANTA KUMA: Ina iya barin jam’iyyar APC – Gwamnan jihar Kwara
“Na yarda da abunda tsohon shugaban kasa Jonathan yakecewa kudirinsa bai kai darajar jinin yan Najeriya ba. Ina ganin tsigewa na da matukar hatsari ga yan Najeriya.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng