Arziki mai anfani: Dangote ya bayar da kyautar Naira miliyan 300
Shahararren mai kudin nan na nahiyar Afrika kuma dan asalin jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote ya gina tare kuma da damka wani katafaren gini da ya lakume zunzurutun kudi har Naira miliyan 300 ga jami'ar tarayya ta Ibadan domin koyo da koyarwar dabarun kasuwancin zamani.
Haka ma dai fitaccen mai kudin wanda babban daraktan zartaswar rukunin kamfanonin na Dangote, Mansur Ahmed ya wakilta, ya kuma sha alwashin cigaba da kaddamar da ire-iren wadannan ayyukan alherin a kasar baki daya.
KU KARANTA: Ciwo ya kama wadda aka yi wa karin duwawu a Najeriya
A wani labarin kuma, Rahotannin da muke samu daga babban bankin Najeriya yana nuni ne da cewa baitul-malin kasar Najeriya na ta cigaba da raurayewa a watanni uku da suka shude a jere kamar dai yadda alkalumman da suka fitar jiya suka nuna.
Rahoton da babban bankin ya fitar dai a ranar Larabar da ta gabata ya nuna cewa baitul-malin yanzu haka dalar Amurka biliyan 47.303 wanda yake nuna cewa dalar Amurka miliyan 394 ce ta zurare a kwanaki 13 kacal da suka gabata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng