Shugaba Buhari ya halarci taron yaye manyan Sojoji a garin Jaji (Kalli kayatattun hotunan)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron yaye manyan jami'an hukumar Sojin Najeriya na Course 40 wadanda aka horar a kwalegin manyan soji da ke garin Jaji, jihar Kaduna a yau Alhamis, 26 ga watan Yuli, 2018.
An gudanar da wannan taro a babban dakin taro na Danjuma Hall da ke barikin sojin Jaji. Daga cikin wadanda suka halarci wannan taroo sune gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i; mataimakin gwamnan jihar, Barnabas Bala Bantex; da shugaban ma'aikatan gwamnati, Winfred Ewe Ita.
Sauran sune babban hafsan jami'an tsaron Najeriya, Janar Olonisakin; babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai; babbanhafdansojin saman Najeriya, Abubakar Saddique Abba; da babban hafsan sojin ruwan Najeriya, Ibok Ekwe Ibas.
Daga cikin ministoci kuma akwai ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali; ministan harkokin cikin gida, AbdurRahman Dambazzau; karamar ministan kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna.
KU KARANTA: An kori masu tsintar bola daga babban birnin tarayya Abuja
Kalli kayatattun hotunan taron:
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng