Zaben kudancin Bauchi: Dan majalisa a sauya sheka daga APC
Wani dan majalisar jihar Bauchi dake neman tikitin takarar kujerar sanatan Bauchi ta kudu a zaben da za’a gudanar, Aminu Tukur ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya bayyana hukuncin sa na barin jam’iyyar bayan wata ganawa a sakatariyar jam’iyyar kafin zaben fid da gwani a ranar Laraba.
Tukur wadda ke wakiltan mazabar Lere/Bula a ajalisar dokokin jihar yace ya bar ja’iyyar saboda hukuncin da ta yanke na amfani da tawaga a maimakon zabin A4 da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana da farko.
A cewarsa, ya shiga takarar ne nda yake sa ran cewa jam’iyar zata ba da fili ga dukkanin yan takara sannan ta gudanar da zaben fid da gwani a bayyane domin tabbatar da adalci.
Ya kuma yi korafin cewa jam’iyyar ta basa kunya bisa hukuncin tan a gudanar da zaben fid da gwani ba kamar yadda aka tsara da farko ba.
KU KARANTA KUMA: Abunda muka tattauna tare da Buhari – Sanatocin APC
A baya Legit.ng ta tattaro cewa sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wadanda suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Laraba sun ce sun je ne domin bashi tabbacin goyon bayansu.
Sun bayyana cewa sun kuma sanar das hi cewar APC ce keda masu rinjaye a majalisun dokokin kasar har yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng