Burin Dangote daya da ya rage a duniya na sayen Arsenal ya kusa cika

Burin Dangote daya da ya rage a duniya na sayen Arsenal ya kusa cika

- Burin shahararren attajirin Nahiyar Afirka sauran kirin ya cika

- Ansha dai jin yadda Dangoten ke bayyana muradinsa na siyen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal

- Wannan dama na daf da samuwa, kasancewar an fara samun baraka a tsakanin masu hannun jari a cikinta

Mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote ya sake bayyana sha'awarsa wajen ganin ya sayi kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, hakan ya biyo bayan wasu rahotanni da suke nuni da cewa Alisher Usmanov dan kasar Russia wanda yake da hannun jari har kaso 30% a kungiyar na shirin cire hannunsa daga cikinta.

Burin Dangote daya da ya rage a duniya ya kusa cika

Burin Dangote daya da ya rage a duniya ya kusa cika

Wata majiya mafi kusa da Usmanov ta bayyana cewa zai cire hannun jarin nasa ne bisa rashin hadin kai da yake samu daga shugaban kungiyar Stan Kroenke, wajen ganin ya dare kan shugabancin kungiyar.

Da aka bukaci jin ta bakin Alhaji Aliko Dangote ya bayyana sha'awarsa wajen ganin ya sayi kungiyar nan da shekaru biyu masu zuwa.

KU KARANTA: Dangote da kamfanin Fijo za su kafa kamfanin hada motoci a Arewa

Idan ba a manta ba shahararren mai kudin wanda yafi kowa tarin dukiya a Nahiyar Afrikan ya nuna sha'awarsa a shekara ta 2010 wajen ganin ya sayi kungiyar amma masu ruwa da tsaki na kungiyar suka ki ba shi hadin kai.

"Zamu yi kokarin ganin mun sake neman sayan Arsenal a shekara ta 2020 ko da kuwa wani zai saye ta zamu gwada sa'ar mu" Dangote ya bayyanawa manema labarai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel