A karshe APC tayi magana kan ficewar gwamnan Benuwe daga jam’iyyar
- Jam’iyyar APC ta bayyana matsayin kan sauya shekar Samuel Ortom
- Ta bayyana cewa sauya sheka yazo mata a matsayin bazata
- Amma duk da yawaitar ficewar ake daga cikinta, APC tayi kira ga mambobin da su kwantar da hankulansu
Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta bayyana cewa tayi mamaki matuka dangane da ficewar gwamnan jihar Benuwe daga cikinta zuwa PDP, sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Malam Bolaji Abudullahi ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a Abuja.
Uwar jam’iyyar ta kuma habarto irin kokarinda da shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole yayi domin ganin ya sasanta rikicin cikin gidan da gwamnan ya zayyana na damunsa a jihar tasa, inda ya ce, “Gwamnan ya bar wajen taron sulhun da akai yana mai gamsuwa da matakin da aka dauka don sulhunta su. “A don haka ne da muka ji labarin ficewarsa mu kayi matukar mamaki”.
APC ta dada jadda matsayinta na girmama ra’ayin duk wani dan kasa domin yana da ikon shiga duk jam’iyyar da tayi masa, amma tana fatan duk wadanda suka sauya shekar zasu sauya tunaninsu kan matakin da suka dauka.
KU KARANTA: Wasu Gwamnonin da ke shirin canza shekar siyasa a Najeriya
Bolaji Abudullahi ya shaida cewa duk da matakin da gwamnan ya dauka na komawa PDP har yanzu suna ganin lokacin yin sulhu bai kure ba, sannan ya sake nanata aniyar jam’iyyar na cigaba da bibiya domin hakurkurtar da fusatattun mambobinta a fadin kasar nan matukar dai sun yarda ayi sulhun.
A baya dai kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa a ranar 29 ga watan Yulin da muke ciki ne gwamnan jihar Benuwen Samuel Ortom ya bayar da tabbaci ga jam’iyyar APC na cigaba da zama a cikin jam’iyyar bayan da yayi ikirarin daga masa jan kati da jam’iyyar APC a jiharsa yayi.
Gwamnan ya sanar da ficewarsa a hukumance daga jam’iyyar ta APC zuwa PDP a jiya 25 ga watan Yuli a fadar gwamnatin jihar dake Makurdi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng