Mun yiwa 'yan Najeriya 31m shaidar 'Yan 'Kasa - NIMC

Mun yiwa 'yan Najeriya 31m shaidar 'Yan 'Kasa - NIMC

Hukumar tabbatar da shaidar dan kasa ta Najeriya watau NIMC (National Identity Management Commission), ta bayyana cewa ta yiwa fiye da 'yan Najeriya Miliyan 31 rajista dake tabbatar da shaidar su ta kasancewar su 'yan kasa.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban reshen sadarwa na hukumar, Mr Loveday Chika, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar nan na Abuja.

Chika yake cewa, wannan shine adadi na yara da manya da hukumar ta tabbatar da su a matsayin 'yan kasar Najeriya, inda adadin yara da hukumar ta tabbatar da shaidar su ya kai kimanin 255, 794 cikin shekaru goma sha daya da kafuwar ta.

Shugaban hukumar NIMC; Engr. Aliyu A. Aziz
Shugaban hukumar NIMC; Engr. Aliyu A. Aziz

Sai dai hukumar ba ta bayar da katin shaidar dan kasar ga Yara wanda suke kasa da shekaru 16 na haihuwa, inda ake sa ran karuwar adadin su da hukumar za ta yiwa rajista sakamakon hutun makarantu dake gabatowa kamar yadda Mista Chika ya bayyana.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta tursasa Ma'aikata amfani da Jiragen ta yayin sufuri

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar za ta gabatar da katin shaidar haihuwa ga yaran ne da ta yiwa rajista a duk sa'ilin da suka kai shekaru 16 da haihuwar su.

Kazalika, hukumar tana shawartar al'ummar kasar da ba su yi rajisatar ba akan sun garzaya cibiyoyin su na kur kusa domin tabbatar da shaidar su. Wannan shaida za ta taimaka kwarai da aniyya wajen ribatar wasu hidimomi na gwamnatin musamman bude asusun ajiya a bankunan kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng