Lokaci yayi da ya kamata a tsige Buhari – Inji Femi-Fani Kayode

Lokaci yayi da ya kamata a tsige Buhari – Inji Femi-Fani Kayode

- Wani tsohon ministan tarayya lokacin tsohon shugaban kasa Obasanjo yayi kira da a tsige Shugaban kasa Buhari

- A makon da ya gabata ne ma wani babban malamin addini ya bukaci shugaba Buhari da yayi murabus

- Ana kukan cewa Shugaban Kasar ya gaza magance matsalar tsaron da ta addabi yankunan kasar nan

Biyo bayan ficewar ‘yan majalisar dattawa 15 daga jam’iyyar APC, inda 14 daga ciki suka koma PDP, sai ga shi tsohon ministan al'adu da yawon bude ido na kasa watau Femi Fani Kayode yana taya daukacin al'ummar kasar nan tare da shugabancin majalisar dattawan murna bisa wannan al'amari mai kama da juyin mulkin siyasa da ya faru.

Lokaci yayi da ya kamata a tsige Buhari – Fani Kayode
Femi Fani Kayode

Cikin wani sakon taya murna da ya fitar a shafinsa na tuwita ya bayyana cewa yanzu haka jam’iyyarmu ta PDP ce ke da rinjaye a zauren majalisar dattawa, saboda haka yana fatan makamancin irin hakan zai kasance a takwararta ta majalisar wakilai. Domin hakan zai bayar da cikakkiyar damar tsige shugaba Buhari daga kan mulkin kasar nan.

KU KARANTA: Fadan karshe: Jamiyyar PDP ta baiwa Saraki, Dogara, Tambuwal da Kwankwaso wa'adin mako biyu su yanke shawara

“Lokacin Shugaba Buhari da jamiyyar APC ya zo karshe, domin kuwa gaf su ke da sauka daga mulkin kasar nan, kuma kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta ICC tana jiransu domin garkamesu. Don a tarihin kasar nan ba'a taba samun shugabancin da aka kashe al'umma ba kamar wanann".

A karshen jerin sakonnin nasa ta tiwita ya bayyana cewa shugabancin Adams Oshiomhole a matsayin marar nasara kuma na kaddara mara kyau ga jam’iyyar, domin kuwa Rotimi Amaechi da Chris Ngige sun dade da bayyana hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel