An yi ram da wanda yake kerawa Barayi da 'Yan fashi bindigogi

An yi ram da wanda yake kerawa Barayi da 'Yan fashi bindigogi

- Karyar wani tsohon mai kerawa miyagu makamai ta kare

- Tsohon dai ana zarginsa da samar da masa'antar harhada sabbi da gyara tsoffin makamai ga masu aikata muggan laifuka

- Tuni dai shi da abokan harkyallarsa sun shiga hannun jami'an tsaro

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta damke wani mutum mai shekaru 72 da haihuwa Obi Benjamin a kauyen Omuoma dake karamar hukumar Ihiala, bisa laifin kafa ma’aikatar kera bindigogi da gyaransu ga masu aikata laifuka.

Dubun wani tsohon najadu mai kerawa barayi da yan fashi bindigogi ta cika

Dubun wani tsohon najadu mai kerawa barayi da yan fashi bindigogi ta cika

Bayan cafke mai laifin an samu bindigogi a masana'antar ta shi ta gyaran bindigu, sannan bayan ya shiga hannu ya shaidawa majiyarmu cewa yana daga cikin 'ya'yan kungiyar maharban garin, kuma yana gyarawa maharba bindigunsu.

Garba Umar wanda shi ne shugaban hukumar ‘yan sanda na jihar, ya bayyana nasarar da shelkwatar ‘yan sandan tayi wajen damke wasu ‘yan kungiyar asiri.

Ya kara da cewa sun samu bayanai daban-daban dangane da aikata laifuka da suka shafi fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma addabar ‘yan kungiyar asiri, wanda suka samu umarnin shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris don ganin an shawo kan matsalar.

KU KARANTA: An yi zazzafar musayar wuta tsakanin Boko Haram da Sojojin Najeriya, kowanne bari sunyi rashi

Kwamishinan ya ce "Bayan samun bayanan sirri ne jami'anmu na SARS suka kai sumame inda suka damke wani matashi dan shekara 25 mai suna Ojiakor Chike a karamar hukumar Ihiala, wanda yayi kaurin suna wajen aikata miyagun laifukan da suka hada da fashi da makami, aiki da ‘yan kungiyar asiri da sauran muggan laifuka".

"A cigaba da binciken da ake yi ne muka yi nasarar sake damke wasu wanda abokan aikin nasa ne masu suna; Izuchukwu Ikueze mai shekaru 25, Nwabueze Ikwueze mai shekaru 27, Chukwudi Obi mai shekaru 30, sai kuma Tochukwu Obi da Cheta Obi, wanda dukkaninsu yanzu suna hannunmu".

"Ta haka ne muka samu bayanai har ta kai ga mun damke Obi Benjamin wanda bashi da wani aiki sai kerawa masu laifin bindigogi. Abin mamaki ma shi ne ya maida wajen tamkar ma'aikatar kayan gyara da kera makamai daban-daban ciki har da bindigogi da muka samu, sai akwatin harsashi da sauran kayan aiki." Garba Umar ya tabbatar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel