Za’a samu karin masu sauya sheka a majalisar wakilai – Dan majalisa
Wani dan majalisar wakilai, Abdulrazak Atunwa, wadda a kasance daga cikin mutane 36 da suka sauya sheka daga jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a ranar Talata, yace akwai Karin yan majalisa da za su bar jam’iyyar a makonni masu zuwa.
Da yake zantawa da manema labarai tare da wasu masu sauya sheka da suka koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atunwa yace sauya shekar da akayi a ranar Talata, 24 ga watan Yuli na sharan fage ne.
Ya bayyana cewa jama’a su zuba idanu domin wasu mambobi da dama sun nuna ra’ayin sauya sheka daga jam’iyyar.
Atunwa ya bayyana cewa APC jam’iya ce da suka yi wahala da ita saboda mutane daga jam’iyyu daban-daban sun shigo ta sannan suka yi kamfen har aka kafa gwamnati a 2015.
KU KARANTA KUMA: Yayinda yan majalisa da yawa suka sauya sheka a APC, gwamnoni sun yunkura domin ceto jam’iyyar
Ya ce jam’iyyar tad aura kanta a kan hanya mara bulle wa, saboda haka ne suka barta domin nemawa jama'a mafita.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng