Hukumar ‘yan sanda tayi nasarar damke ‘Yan fashi 11 a Jihar Ribas

Hukumar ‘yan sanda tayi nasarar damke ‘Yan fashi 11 a Jihar Ribas

- Jami'an 'yan sanda sun samu gagarumar nasarar damke wasu rikakkun 'yan fashi

- 'Yan fashin dai sunyi kaurin suna wurin yin garkuwa da mutane da sace motoci

A iiya ne rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Rivers suka yi holar wasu wadanda ake zargin ‘yan fashi da makami ne tare da aikata miyagun laifuffuka har su 11.

Babbar nasara ga hukumar ‘yan sanda, sun damke ‘yan fashi 11
Babbar nasara ga hukumar ‘yan sanda, sun damke ‘yan fashi 11

Laifuffukan da ake tuhumarsu da su sun hada da garkuwa da mutane, fashi da makami tare da sace motocin jama'a.

KU KARANTA: Dole ne Bukola Saraki ya kai kansa ga ‘yan sanda - In ji sufeton ‘yan sanda na kasa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Rivers Zaki Ahmed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Fatakwal, inda ya tabbatar da cewa ‘yan sandan SARS ne su ka yi nasarar damke wadanda ake zargin a watan da ya gabata, kuma sun kammala bincike akan laifukan da su ka aikata.

"An samu motoci 15 tare da bindigogi 11 da kuma adduna guda 40 sai kuma gatari guda 4" in ji kwamishinan ‘yan sandan na jihar Rivers.

Daga karshe shugaban ‘yan sandan ya tabbatar da cewa aikin dan sanda aiki ne da zai bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyin al'umma a kowane lokaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng