Bayan fitar Kwankwaso daga jamiyyar APC ko Gwamna Ganduje zai cire jar Hula (Rahoto)
- Yau dai anyi ta ta kare tsakanin tsohon gwamna Kwankwaso da APC
- Yanzu kuma ido ya koma kan gwamnan Kano Ganduje ko zai yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda
Ga dukkan wadanda ke bibiyar al'amuran siyasar jihar Kano ya kwana da sanin tsattsamar dangantakar da ke tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar mai ci yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Kafin abubuwa su lalace dai Kwankwaso da Ganduje sun kasance tamkar 'yan biyu ta fannin siyasa tun dawowar mulkin dimokuradiya a shekara ta 1999.
Sau biyu dai Ganduje ya na kasancewa mataimakin gwamna Kwankwaso, ba wanda zai yi tunanin za a samun baraka a tsakanin su, amma Hausawa na cewa zo mu zauna tamkar zo mu saba ne.
Bayan zama bisa karagar mulki da gwamna Ganduje ya yi, sai aka fara samun baraka nan da can tsakaninsa da tsohon mai gidan nasa. Abu kamar wasa wai karamar magana ta zama babba, domin kuwa rikicin siyasar sai da ya kai ga kakkabe manyan hadiman tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso daga kunshin gwamnatin Ganduje baki daya.
KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Sanatoci 15 sun sauya sheka daga APC
Tare da daukar wani mataki da ya dakatar da zuwansa Kano saboda dalilan tsaro wanda ya haramtawa madugun darikar ta Kwankwasiyya kawo ziyara jihar Kano domin ganawa da magoya bayansa.
To amma sai dai adon jar hula tare da fararen kaya wannan shi ne alamar kwankwasiyya da dukkanin wani mai akida ko amincewa da tsarin Kwankwasiyya ke amfani da shi, duk wanda yake da wannan akidar zaka same shi da jar hula kusan ko yaushe sanye akansa.
Duk da irin wannan rikicin da ake yi tsakanin Kwankwaso da Ganduje, hakan bai sanya gwamna Ganduje ya cire jar hula ba, duk da cewa magoya bayan Kwankwasiyya sun yi kira akan ya cire alamar Kwankwasiyya daga kansa, bisa zarginsa da yin butulci ga tsohon mai gidansa a siyasance.
Biyo bayan wutar rikicin shugabanci da ta dade tana ruruwa a jam'iyyar APC, Sai ga shi yau an wayi gari da ficewar jagoran darikar Kwankwasiyyar na kasa baki daya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso daga jamiyyar APC zuwa PDP.
Abin Tambaya a nan shi ne tun da yanzu maganar sulhu ta kare, shin gwamnan zai karasa cire jar Hula daga kansa, Ko kuwa duk da an raba gari a tsakaninsa da mai gidansa a siyasa zai cigaba da dakon sanya alamomin kwankwasiyya?
Al'ummar Jihar Kano dai sun zuba idanu domin ganin ko gwamna Gandujen zai cire jar Hula ya koma sanya wadda ransa yake so.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng