Dole ne Bukola Saraki ya kai kansa ga ‘yan sanda - In ji sufeton ‘yan sanda na kasa
- Wata sabuwar sanarwa da 'yan sanda suka fitar, sun ce tilas ya kai kansa don amsa tambayoyi
- Wannan sanarwa na zuwa bayan da Sarakin ya surarewa kamun da 'yan sandan su kayi niyyar yi masa da safiyar yau
Rundunar yan sandan kasa sun nanata kudurin cewa lallai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya gurfana a gaban rundunar ‘yan sanda domin amsa tamboyi.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘Yan sanda na kasa DCP Jimoh Moshood ya rabawa manema labarai a ranar Talatar nan, sanarwar ta kara da cewa tilas ne Saraki ya kai kansa wurin rundunar domin amsa tambayoyi masu alaka da fashi da makamin da aka yi a wani banki da ke garin Offa da ke jihar Kwara.
KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga - jigan ta guda 4
Sanarwar ta bayyana cewa tun da farko dama an taba gayyatarsa domin binciken da ake yi akan yadda wani dan fashi ya bayyana Sarakin a matsayin wanda ya ke daukar nauyinsu.
"Duk da ya samu takardar gayyatar amma sai yayi biris da gayyatar, sanarwar ta jaddada cewa lallai Bukola Saraki da ya gabatar da kansa a sashen binciken laifuffuka da ke Guzape a shiyyar Asokoron dake Abuja".
A karshe sanarwar ta jaddada Daukar mataki ga dukkanin wani wanda yaki bin doka a fadin kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng