Yadda wata hatsabibiyar yarinya ta kitsa sace kanta tare da karbar kudin fansa daga mahaifin ta a Najeriya

Yadda wata hatsabibiyar yarinya ta kitsa sace kanta tare da karbar kudin fansa daga mahaifin ta a Najeriya

Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a rundunar jihar Legas sun bayar da labarin yadda suka samu nasarar cafke wata hatsabibiyar yarinya mai suna Dorcas Adilewa da ta da kitsa sace kanta tare da karbar kudin fansa zaga wurin mahaifin ta mai suna Raiwo Adilewa.

Ita dai Dorcas din, jami'an 'yan sanda sun cewa wata kawar ta ce mai suna Ifeoluwa itace ta bata mafaka a gidan da take duk dai a cikin garin Legas din.

Yadda wata hatsabibiyar yarinya ta kitsa sace kanta tare da karbar kudin fansa daga mahaifin ta a Najeriya
Yadda wata hatsabibiyar yarinya ta kitsa sace kanta tare da karbar kudin fansa daga mahaifin ta a Najeriya

KU KARANTA: Dadin bakin Buhari ba zai hana mu ficewa daga APC ba - Su Buba Galadima

Legit.ng ta samu cewa 'yan sandan sun ce sun shiga maganar ne tare da fara binciken lamarin lokacin da mahaifin nata ya kai masu karar cewa wasu sun sace masa diya kuma har ma sun bukaci ya biya su Naira dubu dari 6.

Sai dai bayan dogon bincike da 'jan sandan suka yi sai suka gano ba haka bane yarinyar itace ta kitsa sace kan ta domin ta karbi kudin daga wurin mahaifin nata.

Sai dai ita yarinyar tace ta yi hakan ne domin ta samu ta biya kudin makarantar ta da tace uban nata yaki biya yace bai da kudi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng