Ambaliyar ruwa: Bayan cigaba da lalube an sake gano gawar mutane 10 a Katsina

Ambaliyar ruwa: Bayan cigaba da lalube an sake gano gawar mutane 10 a Katsina

- Al'ummar jihar Katsina na cigaba da zaman makoki bayan ambaliyar ruwan da ta afku

- Ambaliyar ruwan dai ta faru ne sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka

- Sai dai kuma bayan gawarwakin da aka samu tun farko ciki har da ta wata sabuwar amarya, yanzu haka an sake gano wasu daban

A yau Litinin Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir ya bayyana rahotan sake samun karin gawar mutane 10 da suka rasu a dalilin ambaliyar ruwan da ya auku a garin Jibiya wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da salwantar dukiyoyin jama'a.

Ambaliyar ruwa: Bayan cigaba da lalube an sake gano gawar mutane 10 Katsina
Ambaliyar ruwa: Bayan cigaba da lalube an sake gano gawar mutane 10 Katsina

Ambaliyar ta faru ne a ranar 15 ga watan Yulin da muke ciki, inda mutane sama da 44 suka rasa rayukansu sannan gidaje sama da 500 suka rushe.

Mai martaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake cigaba da karbar gaisuwar mutuwar tsohon shugaban hukumar ‘yan sanda ta kasa baki daya Alhaji Ibrahim Coomassie, inda ya bayyana cewa tuni an binne gawarwakin da aka sake samowa.

"Mazauna yankin sun kai karafi ga Dagacin yankin Jibiya, wanda nan take ya bada umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin abinda ke warin, bayan bincike na tsawon wasu sa'o'i sai aka gano gawar wasu mutane har 10." Sarkin ya bayyana.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa tayi sanadin mutuwar mutune 13, muhalli 17,000 sun salwanta a Nijar

Sannan ya kara da cewa "Dagacin daga bisani ya sanar dani abinda ake ciki domin hada adadin lissafin mutanen da aka rasa sakamakon wannan annoba ta ambaliya da ta auku".

Sarkin ya bukaci jama'a da su saka jihar a cikin addu'o'i domin neman kariya daga wata musiba makamciyar wannan.

Ambaliyar ruwa: Bayan cigaba da lalube an sake gano gawar mutane 10 Katsina
Ambaliyar ruwa: Bayan cigaba da lalube an sake gano gawar mutane 10 Katsina

Haka kuma ya bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda al'amarin ya rutsa dasu 'yan kasuwa ne wadanda sun rasa dukiyoyinsu da yawa.

A don haka ne yayi kira ga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran jama'a da su taimake su saboda basu da wata hanya da zasu maye gurbin asarar da suka yi domin ganin sun dawo da kafarsu kan harkokin kasuwancinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng