Buba Galadima hawainiyarka ta kiyayi ramar Buhari – Martani mai zafi daga masoya Buhari
- Da alama sukar da ake wa shugaba Buhari bata yiwa wasu dadi
- Har ta kai ga sun hada kai sun fitar da sanarwar gargadi kan cewa a daina
Wasu gamayyar kungiyoyin matasa karkashin inuwar Democratic Youth Congress for Buhari (DYC4Buhari) sun jan hankalin shugaban tsagin jamiyyar R-APC Buba Galadima akan irin kalubalantar shugaba Muhammad Buhari da yake yi.
Jawabin hakan yana cikin wata sanarwar da inuwar matasan karkashin jagorancin Hon. Kassim Muhammad Kassim wanda dan majalisar dokoki ne daga jihar Nasarawa ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan abin kaico ne a ce mutumin da ke a matsayin dattijo a kasar nan amma kuma a same shi yana irin wadannan maganganun.
KU KARANTA: Jan kunne: Idan Buhari na daukar raini, toh ni bani daukar raini – Inji shugaban APC Oshiomole
Ya kara da cewa ikirarin da Buba Galadima yake yi, akan shi ne sanadin nasarar shugaba Muhammad Buhari a zaben shekara ta 2015 ba haka abin ya ke ba, domin al'ummar kasar nan sun zabi shugaba Muhammad Buhari saboda nagartarsa da kuma irin gaskiyar da ya ke da ita.
Abin da ya rage yanzu shi ne, ko Buba Galadiman zai daina zazzafar sukar da yake yawaita yiwa shugaba Muhammadu Buhari ko zai cigaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng