Leah Sharibu bata bar addinin kirista ba – Mama Boko Haram
Misis Aisha Wakil, wacce aka fi sani da Mama Boko Haram ta bayyana cewa Leah Sharibu bata bar addininta na Kirista ba.
Wakil ta bayyana hakan ne yayin da ta sanar da cewa tana aiki tare da kwamitin bayar da taimako na kasa da kasa wajen ceto Leah Sharibu.
Leah ta kasance Kirita guda a cikin yan matan makarantar Dapchi 112 da yan ta’addan Boko Haram suka kama a jihar Yobe.
An rike Leah ne sakamakon kin barin addinin musulunci, yayinda Boko Haram suka dawo da sauran yan matan gida ga iyayensu.
KU KARANTA KUMA: R-APC: Ina baccina harda munshari – Oshiomhole
Aisha ta bayyana cewa ta damu matuka akan rashin sakin Leah day an Boko Haram suka ki yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng