Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano

Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano

- Ganuwar Kano da ta shafe shekaru daruruwa na fuskantar barazanar shafewa daga tarihi

- 'Yan siyasa da shafaffu da mai wasu marasa kishi da rashin sanin muhimmancinta ne ke kan gaba wajen yunkurin maye gurbinta da nasu aikin

Duk da cewa Ganuwa a garin Kano aba ce mai dimbin tarihi dake kawata birnin tun a karnin da aka gina su har kawo yau, sai dai za’a iya cewa a yanzu lamarin ya sha bambam bisa yadda wasu mutanen gari da ‘yan siyasa ke neman kawo karshen Ganuwar.

Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano
Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano

Wani mazaunin yankin kofar Na'isa mai suna Falalu Musa, ya koka game da yadda ake nuna halin ko in kula da Ganuwar musamman ta bangaren Kofar Na'isa zuwa kan titin B.U.K.

Inda ya bayyana cewa wasu sun mayar da wani bangare nata wajen zubar da juji, wasu kuma sun mayar da ita wurin fakewa don yin shaye-shaye, yayin da wasu yan siyasar suka mayar da kewayenta abin sayarwa ko kyauta ga ‘yan uwansu yan siyasa wanda hakan zai iya kawo karshen dimbin tarihin dake tare da Ganuwar.

Shi ma ta bangarensa shugaban gidan ajiye kayan tahiri na Kano (Gidan Makama) Mustapha Bachaka ya koka kan yadda "Gine-ginen ginin Ganuwar mai tarihi kusan kashi 80% na shi aka rushe sa zuwa wani abu na daban wanda wannan abun damuwa ne".

Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano
Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano

KU KARANTA: Ana zaton wuta a makera: An kama jami’an SARS 4 da laifin fashi da makami

Wannan gini na ganuwa ya samo asali ne tun a karni na 11, wanda abu ne mai daukar hankali musamman ga mutane masu yawon bude ido da kuma sanin tarihi. An dai gina ta ne da nufin kare kai daga abokan gaba, ganuwar tana dauke da kofofi a kalla guda 13 da suka kewaye babban birnin na Kano.

Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano
Yadda 'yan siyasa da wasu shafaffu da mai ke shirin ganin karshen dadaddiyar Ganuwar Kano

Aliyu Abdu wanda shi ne shugaban hukumar adana kayan tarihi na kasa reshen jihar Kano, shi ma ya bayyana damuwarsa inda ya ce "Tabbas laifin gwamnati ne saboda ita ce take daukar filaye take bawa magoya bayanta ko ta sayar a wannan waje mai dimbin tarihi, wanda su kuma suke amfani da wannan dama wajen rushe ire-iren wadannan gurare". Kamar yadda Jaridar Vanguard ta rawaito.

Abdu ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu hukumar ta nada wakilai domin wani aikin gani da ido don sanin halin da wadannan gine-gine na tarihi ke ciki, wanda yace ba zasu yi kasa a guiwa ba dan ganin an kawo karshen wannan matsala da kayan tarihin ke fuskanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng