A rana ta yau a shekarar 2014 aka kaiwa Sheik Dahiru Bauchi harin Bam a Kaduna
Akalla mutane 82 sun hallaka a jihar Kaduna ranan, wasu da yawa kuma sun jikkata yayinda yan kunar bakin waken suka kai harin Bam babban malami, Sheik Dahiru Usman Bauchi a farfajiyar Murtala Square inda akayi taro.
Wannan harin Bam ya faru ne misalin karfe 12:30 na ranan a titin Isa Kaita bayan babban malamin addinin ya gabatar da jawabi a taron kungiyar yan darikar Tijanniya.
Hukumar yan sanda ta bayyana cewa mutane 25 ne suka rasa rayukansu amma mutanen da suka shaida harin sun ce akalla mutane 40 suka hallaka.
Wani wanda ya shaida harin mai suna Isa Sai’du ya bayyanawa manema labarai cewa: “Ina farfajiyar Murtala Mohammed Square inda Sheiku Dahiru Bauchi ya yi mana wa’azi. Kana kuma ina cikin wadanda suke rakashi gida bayan taron.”
"Kawai sai wani mutum ya nufo a guje kan babur rike da jaka a hannunsa. Ya na gudun ganganci kuma wani jami’n tsaronmu ya yi kokarin tsayar da shi amma yaki. Sai yayi kokarin karasowa kusa da motan da Shehi ke ciki amma aka hana shi.”
KU KARANTA: A ranan irin ta yau aka kaiwa Buhari harim Bam a Kaduna
“Da ya dage sai ya zo sai aka tureshi daga kan hanya ya fada kwata, kawai sai Bam ya tashi. Jikin sheik Dahiru Bauchi na rufe da jinin wadanda ke kareshi. Na rantse da Allah na kirga gawawwaki 41 da kaina. Wanna shine abu mafi tsoro da na shaida a rayuwata.”
Awa biyu da faruwan wannan hari aka kaiwa Janar Muhammadu Buhari hari Bam misalin karfe 2:30 na ana bayan shugaba Buhari yayinda shugaba Buhari ya nufi tafiya Daura a karkashin gadar unguwar Kawo.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng