Jerin mutane 19 da suka rike mukamin ‘Babban sufetan Yansandan Najeriya’

Jerin mutane 19 da suka rike mukamin ‘Babban sufetan Yansandan Najeriya’

Aikin Yansanda wani ginshiki ne na tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a ko ina a duk fadin Duniya. A Najeriya kuwa, tun bayan samun yancin kai daga shuwagabannin mulkin mallaka a shekarar 1960, an yi Babban sufetan Yansanda guda goma sha tara.

Legit.ng ta ruwaito dan Najeriya na farko da ya fara rike mukamin babban sufetan Yansandan Najeriya shi ne Louis Edet, wanda ya dare wannan mukami a shekarar 1964, har zuwa shekarar 1966, inda yayi ritaya a shekarar 1966.

KU KARANTA: Kiran ruwa babu lema: Fusatattun matasa sun halaka dakarun Soji guda 3

Sauran manyan sufetan Yansandan Najeriya sun hada da;

2-Kam Salem 1966-1975

3-Muhammadu Dikko Yusuf 1975-1979

4-Adamu Suleiman

5-Sunday Adewusi 1981-1983

6-Etim Inyang 1985-1986

7-Muhammad Gambo Jimeta 1986-1990

8-Aliyu Attah 1990-1993

9-Ibrahim Coommassie 1993-1999

10-Muslim Smith 1999-2002

11-Mustafa Adebayo Balogun 2002-2005

12-Sunday Ehindero 2005-2007

13-Mike Mbama Okiro 2007-2009

14-Ogbonna Okechukwu 2009-2010

15-Hafiz Ringim 2010-2012

16-Mohammd Dahiru Abubakar 2012-2014

17-Suleiman Abba 2014-2015

18-Solomon Arase 2015-2016

19-Ibrahim Idris Kpotun 2016- zuwa yanzu

Da wannan za a iya gane cewa Kam Salem ne babban sufetan Yansanda mafi dadewa a mukamin, tun daga shekarar 1966 zuwa 1975, shi ya jagoranci rundunar Yansandan Najeriya a lokcin da aka yi yakin basasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng