Gwamnati ta gina gidan kallo don kawar da akidar Boko Haram a tsakanin matasa
Gwamnatin karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe ta shiga aikin gyaran gidajen kallo, inda ya fara da wani gidan kallo dake kauyen Garin gada wanda take sa ran hakan zai taimaka wajen yaki da mummunan akidar Boko Haram.
Shugaban karamar hukumar, wanda ya samu wakilcin guda cikin kansilolinsa, Dawa A Doma ya bayyana cewa wata kungiyar sake farfado da yankin Arewa maso gabasa, NERI ce ta samar da kudaden da aka yi wannan gyara.
KU KARANTA: Mai laya ya kiyayi mai zamani: Jaruman Kannywood 4 da tauraruwarsu ke haskawa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito manufar gina wannan gidan kallo itace don ilimantar da matasa hadduran dake tattare da shaye shaye, akidar Boko Haram da ma sauran miyagun dabi’u, kasila Doma yace za’a dinga haska fina finai masu ma’ana, da zasu karantar da matasa muhimmancin zaman lafiya.
“Muna sa ran wannan cibiyar kallo za ta hada kan matasanmu, tare da saitasu akan turbar ciyar da yankinmu gaba, haka zalika cibiyar na da muhimmanci, musamman duba da yadda matasa ke zuwa wurare masu nisa don kallon gasar cin kofin Duniya da aka kammala.” Inji shi.
Bugu da kari an jona gidan kallon da na’urar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, da kuma famfon tuka tuka, wanda hakimin garin, Lawan Abubakar ya bayyana su a matsayin abubuwan da suke tabbatar da zaman lafiya ya samu a yankin.
Daga karshe ya yi alkawain kafa wata kwamitin jajirtattun mutanen garin da zasu dinga sa ido akan wadannan ayyuka, da kuma kula dasu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng