Ba dadin ji: Boko Haram sun yanka mutane 18 sun yi awon gaba da mata 10

Ba dadin ji: Boko Haram sun yanka mutane 18 sun yi awon gaba da mata 10

- Kasashen Nijar da Chadi dake Makwabtaka da Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro

- Wasu rahotannin da kamfanin dillancin labarai na kasa na AFP ya rawaito wata barna da mayakan Boko Haram su kayi a can

Rundunar Sojin kasar Chadi ta ce mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 18 a wani hari da suka kai kan wani kauye kudu da garin Daboua, da ke kan iyakar kasar da jamhuriyar Nijar.

Ba dadin ji: Boko Haram sun yanka mutane 18 sun yi awon gaba da mata 10
Ba dadin ji: Boko Haram sun yanka mutane 18 sun yi awon gaba da mata 10

Majiyar Sojin kasar wadda ta fitar da sanarwar a yau lahadi, ta ce ta’addan na Boko Haram sun kai harin ne tun a ranar Alhamis da ta gabata, inda suka sace mata 10 tare da jikkata mutane 2.

KU KARANTA: Jihar Zamfara zata samu sauki: Masu garkuwa da mutane 4 da makamasu sun shiga hannun ‘yan sanda

A watan Mayun da ya gabata, akalla mutane 6 ne suka hallaka a wani hari da mayakan na Boko Haram suka kai kan wani shingen binciken ababen hawa na sojin kasar ta Chadi.

Harin dai ya rutsa ne da wasu jami’an gwamnatin Chadi 4 da kuma wani soja daya.

Haka zalika a jiya Asabar 21 ga watan Yuli na 2018, rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da samun nasarar hallaka wasu mayakan Boko haram 10, bayanda suka kai wa daya daga cikin sansanoninta hari a yankin kudu maso yammacin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng