Jihar Zamfara zata samu sauki: Masu garkuwa da mutane 4 da makamasu sun shiga hannun ‘yan sanda

Jihar Zamfara zata samu sauki: Masu garkuwa da mutane 4 da makamasu sun shiga hannun ‘yan sanda

- 'Yan sanda sun samu gagarumar nasara kan wasu 'yan ta'adda a jihar Zamfara

- Ana zargin wadanda aka kama da kwarewa wajen yin garkuwa da mutane da fashi da makami

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wasu mutane hudu, da take zarginsu da yin garkuwa da mutane.

Kakakin ‘yan sandan jihar Muhd Shehu, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a maboyarsu da ke Zawuyya, Badarawa da kuma Birnin-yero a kananan hukumomin Gusau da Shinkafi.

Daga cikin makaman da aka samu a tare da wadanda ake zargi akwai, bindigogi kirar gida guda 16, sai kuma adduna biyar.

KU KARANTA: Iftila’in gobara ya kone shaguna a wata babbar Kasuwa a Kano

Wadanda aka kama din dai ana zarginsu ne da aikata aiyukan ta'addanci wadanda su ka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma kisan gilla da ya addabi jihar ta Zamfara.

Ya bayyana cewa Idan za'a iya tunawa dai a ranar 15 ga watan Yuli ne, rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarar kama mutum saba'in da ake zarginsu da hannunsu wajen aikata laifuffukan da su ka addabi jihar.

Wanda tuni an gurfanar da mutune 43 gaban kuliya yayin da sauran 29 su ke hannun rundunar ‘yan sandan domin yayin da suke zurfafa bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel