Jerin sunayen masu tsaron raga 5 da suka fi tsada a Duniya baki daya (Hotuna)
1- ALLISON BARKER: Wannan dan wasa dan kasar Brazil yana taka leda ne a kungiyar kwallon kafa ta AS Roma. Barker ya kasance hazikin mai tsaron raga, wanda jajircewarsa tasa kungiyoyi da dama dagewa don ganin sun dauke shi. Amma daga karshe kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool ce ta yi nasarar daukarsa akan kudi har £67, wanda hakan yasa ya zamo mai tsaron raga na farko da yafi kowanne tsada a tarihin kwallon kafa.
2- EDERSON: wanda shi ma dan kasar Brazil ne ya sauya sheka ne daga kungiyar kwallon kafa ta Benfica zuwa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City akan kudi £35. Bayan rattaba hannu a kungiyar ya zamo mai tsaron raga na farko wajen nuna kwazo.
3- GAINLUIGI BUFFON: dan wasan dan asalin kasar Italiya ya kasance daya daga cikin jerin masu tsaron raga mafi tsada a Duniya kuma na farko kafin saye Allison Barker da Ederson. Kungiyar Juventus ta sayi mai tsaron ragar ne daga kungiyar kwallon kafa ta Panama a shekara ta 2001 akan kudi £32.6.
KU KARANTA: Dalilai 2 da yasa Faransa zata yi nasara a wasan karshe na kofin duniya yau
4- JORDAN PICKFORD: dan wasan dan asalin kasar England, ya kasance daya daga cikin masu tsaron raga da karansu ya kai tsaiko. Kuma daya daga cikin jerin tsada a duniya. Dan wasan ya sauya sheka ne daga kungiyar kwallon kafa ta Sunderland zuwa kungiyar kwallon kafa ta Everton a shekara ta 2017 akan kudi £30. Pickford ya taimakawa kasarsa ta England zuwa wasan kusa dana karshen gasar cin kofin duniya da aka gama gudanarwa a kasar Russia, wanda kasar tasa ta kare a mataki na hudu a gasar.
5- BERND LENO: wannan mai tsaron raga za a iya cewa shi mafi karancin shekaru a cikin jerin sunayen da aka lissafo. Mai tsaron ragar dan asalin kasar Jamus ya shafe shekaru bakwai yana taka leda a kungiyar kwallon ta Bayer Leverkusen. Kingiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi sayi mai tsaron ragar akan kudi £22 a farkon kakar cinikayyar yan wasa ta bana (2018).
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng