Alakwurra 4 da Buhari ya dauka a 2015 kuma har yanzu bai cika su ba
Kamar kowane dan siyasa, Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zabe a shekarar 2015 ya zagaya jahohin Najeriya tare da kuma ganawa da daruruwan kungiyoyi inda ya yi masu alkawurra da dama idan dai har suka zabe shi.
Duk da dai siyasa daman kamar yadda masu fashin baki da dama kan fada cewa ta gajin rashin cika alkawari, amma talakawan Najeriya da ma al'ummomin kasashen duniya sun yi ammanar cewa shugaba Buhari ya sha ban-ban da sauran 'yan siyasa.
KU KARANTA: Sojin saman Najeriya sun yiwa 'yan Boko Haram luguden wuta
Legit.ng ta samu cewa sai dai kawo yanzu da ya rage saura watanni kadan kacal kafin wa'adin mulkin sa ya kare, akwai wasu muhimman alkawura da ya dauka ya kuma sha alwashin tabbatar da su idan dai har ya lashe zaben sa.
1. Magance rashin tsaro:
Duk da dai a iya cewa gwamnatin sa ta samu nasara sosai musamman ma a yakin da take yi da 'yan kungiyar Boko Haram, har yanzu akwai sauran rina a kaba a sassan kasar.
2. Farfado da tattalin arzki:
Da samun karayar darajar kudin naira tare kuma da hauhawar farashin kayan masarufi da na abinci, masana da dama na ganin yanzu tattalin arzikin Najeriya kara tabarbarewa yayi.
3. Samar da aikin yi ga matasa:
Duba da irin shire-shiren da gwamnatin ta bullo da su da ke da alaka ta kai tsaye ga samarwa matasa aikin yi kamar su shirin nan na N-power da kuma harkar noma, a iya cewa gwamnatin ta kokarta. Amma dai saboda yawan al'ummar kasar, har yanzu rashin aikin yi a tsakanin matasa na nan ba'a magance shi ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng