Attahiru Jega ya fallasa babbar matsalar 'yan siyasar Najeriya
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana babbar matsalar 'yan siyasar Najeriya da cewa su burin su kawai su lashe zabe ba wai su gudanar da sahihin shugabanci ba.
Jega ya bayyana cewa wannan babbar matsalar ta su idan har aka duba itace ummul abasin dukkan koma bayan da kasar ke fama da ita.
KU KARANTA: Buhari baya sona kwata-kwata - Inji wani gwamnan Arewa
Legit.ng ta samu cewa Jega yayi wannan kiran ne a yayin da yake gabatar da makalar sa ga wasu manyan jami'ai na kasar da suke gudanar da karatun su na wani kwas a garin Abuja.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Taraba dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan, Mista Darius Ishaku ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shirya makarkashiyar hana shi tare da wasu gwamnoni 6 sake tsayawa takara a 2019.
Darius Ishaku ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a gidan gwamnatin jihar, garin Jalingo.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng