Kudi N30,000 aka biyani domin sace yan matan Chibok – Kwamandan Boko Haram
Mayinta Modu, wani kwamandan Boko Haram ya bayyana cewa N30,000 aka biyashi a matsayin la’adan shirya yadda aka sace yan matan makarantan Chibok a shekarar 2014.
Modu ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a ofishin hukumar yan sanda da ke Maiduguri, jihar Borno.
Kwamandan Boko Haramun na daga cikin yan kungiyar 22 da hukumar yan sanda suka damke a jihar Adamawa da Borno.
Kwamishanan yan sandan jihar Borno, Damian Chukwu, ya bayyana cewa Modu da wasu bakwai ne suke da hannu cikin sace yan matan.
Dan ta’addan yace sai da sukayi kwanaki da yawa a cikin daji kafin suka mikawa kwamadojin Boko Haram yan matan.
Yace: “An sake yawancin yan matan da muka sace. Dubu talatin aka biya kowannenmu don wannan aiki,”
“Hakazalika, bayan an sake wasu daga cikin yan matan sakamakon cinike da gwamnati, an kara mana tsakanin N30,000 zuwa N60,00.”
KU KARANTA: An ceto wata Jaririya a karkashin Tirela a Kaduna, mahaifiyarsa ce taso kashe shi
Modu yace ya shirya manyan hare-hare a Bama da Gwoza inda rayukan mutane da yawa suka salwanta.
Kana yace ya bada gudunmuwa wajen daukan kananan yara maza da mata da ake amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake a Maiduguri da kuma wasu sassan Arewa maso gabas.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng