Shugaba Buhari ya aika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan maigayi Ibrahim Coomassie
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Katsina da iyalai kan rasuwar tsohon sifeto janar na hukumar yan sanda kuma abokinsa, Ibrahim Coomassie.
Sakon ta’azziyyar shugaba Buhari na kunshe kunshe cikin wani jawabi da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki ranan Alhamis bayan sanarwan rasuwarsa.
Shugaba Buharu ya ce wannan labara na rasuwan shugaban kungiyar Arewa wato Arewa Consultative Forum, ACF ya firgitashi.
Yace: “Najeriya ba zata taba mantawan da irin shugabancin da marigayi Coomassie yayiwa hukumar yan sandan Najeriya ba lokacin da yake sifeto.”
“A madadin gwamnati da mutanen Najeriya, muna rokon Allah ya jikansa, ya rahamcesa kuma karawa iyalansa hakuri,”
IG Coomassie ya rasu ne jiya Alhamis, 19 ga watan Yuli, 2018 a asibitin jihar Katsina inda yayi jinya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng