Gani ga wane: Wani Dansanda da ya amshi cin hanci daga hannun Danfashi ya gamu da tsatstsauran hukunci

Gani ga wane: Wani Dansanda da ya amshi cin hanci daga hannun Danfashi ya gamu da tsatstsauran hukunci

Babbar kotun jihar Oyo ta yanke ma wani Dansanda hukuncin zaman gidan kaso bayan ta kama shi da laifin karbar na goro daga wajen wani kasurgumin dan fashi da aka kama, Badmus Akojode a lokacin da suke bincikensa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kotun ta yanke ma Dansandan ne mai suna Akanmu Kabiru, tare da abokan aikinsa Tajudeen Olalere da Omotosho Lawrence, dukkaninsu akan wannan laifi.

KU KARANTA: Wata budurwa mai Aljanu ta tashi ajin dalibai a jami’ar Usmanu Danfodiyo

A shekarar 2007 ne hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta gurfanar da Yansandan gaban Alkali mai sharia A.I Akintola akan tuhume tuhume guda huus da suka dangancin nema da kuma kabar cin hanci daga yan dan fashin da suke bincikensa.

Lauyan ICPC ya bayyana ma Kotu cewar Yansandan, wanda tuni aka sallamesu daga aiki sun nemi Dan fashin ya biyasu kudi naira dubu dari biyu don su wanke shi daga laifin fashi da makami da ya tafka, inda lauyan yace hakan ya saba ma sashi na 8 (1) (a) da na 26 (1) (c) na dokokin hukumar.

Sai dai Dansandan da ake kara ya musanta tuhume tuhumen, amma duk da haka bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkalin kotun ya bayyana cewa kotu ta kama shi da laifin, don haka ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru uku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel