An ceto wata Jaririya a karkashin Tirela a Kaduna, mahaifiyarsa ce taso kashe shi
- Wata dimautacciyar matashiyar mai jego tayi nufin kashe danta
- Ta jefa Jaririyarne kasan motar Tirela don ta tatsile ta, amma hakanta bai cimma ruwa ba domin kuwa an ceto
An yi nasarar kubutar da wani jariri dan watanni uku da haihuwa daga hannun mahaifiyarsa bayan da ta yi yunkurin kashe sa.
Kwamishinan kula da harkokin mata ta jihar Kaduna ce ta yi nasarar kubutar da jaririn daga mahaifiyarsa mai suna Aisha wadda alamu suka nuna bata cikin hayyacinta.
Aisha wadda ita ce mahaifiyar jaririn tana zaune ne a karkashin sananniyar gadar nan ta yankin Kawo dake jihar ta Kaduna, inda ta ajiye jaririn karkashin tayar babbar mota da nufin ta take yaron a yayin da motar zata tashi.
KU KARANTA: Wani likita ya shiga tasku bayan shararawa abokiyar aikinsa mari
Domin tabbatar da hakan ta faru ne Aisha ta yi ta kokarin ganin ta hana mutane rabar inda jaririn yake, tare da tilastawa direban motar don ganin ya tashi motar.
Wannan lamari ya dauki tsawon lokaci ana yinsa, wanda daga bisani wani fasinja ya kai labarin lamari ga kwamishinan mata, wanda nan take ita da wasu jami'an gwamnati suka dunguma zuwa wajen domin ceto wannan jariri.
Sai dai yayin yi mata tambayoyi, Aisha ta bayyana cewa bata san ya aka yi ta tsinci kanta a jihar ta Kaduna ba, tace rikici da tashin hankalin da ya auku a jihar Taraba ne ya tarwatsa ‘yan uwanta wanda ya zuwa yanzu shekara daya kenan bata san halin da suke ciki ba balle samun labarinsu.
"Sunana Aisha Yau mai shekaru 20 da haihuwa, ni mutuniyar Taraba ce rikici ne ya rabani da yan uwana". Ban san ta wane hali na tsinci kaina a Kaduna ba, amma a lokacin da na gane ina Kaduna sai na tuna da shagon wani saurayina a nan wajen Kasuwan Baici sai dai ban san sunansa ba, wanda shi ne ya min ciki. Daga bisani yace ba nashi bane yaki yarda ya amince da cikin balle ya dauki nauyin kula dani da yaro na. shi yasa na yanke hukuncin kashe jaririn domin gujewa jin kunya".
Jim kadan bayan ganawa da manema labarai, kwamishiniyar kula da harkokin matar ta umarci da akai uwar jaririn asibiti domin duba lafiyarta kafin a maida ta jihar Taraba
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng