Wani likita ya shiga tasku bayan shararawa abokiyar aikinsa mari

Wani likita ya shiga tasku bayan shararawa abokiyar aikinsa mari

- Saurin fushi ya ce je likita cikin matsala bayan marin ma'aikaciyarsa

- Likitan ya mare ta ne a lokacin da hayaniya ta barke a tsakaninsu

- Bayan gurfana gaban alkali, ya musanta zargin da ake masa

Wani likita mai suna Emmanuel Okolo dan shekaru 35 da haihuwa, ya gurfana gaban kotun Majistire bisa laifin sharara marin wata ma'aikaciyar jiyya dake aiki a asibitinsa.

Wani likita ya shiga tasku bayan shararawa abokiyar aikinsa mari
Wani likita ya shiga tasku bayan shararawa abokiyar aikinsa mari

Dan sandan mai gabatar da karar a gaban kotu Moses Oyekanmi, ya bayyanawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata lafin ne ranar Laraba da misalin karfe 2 na dare a asibitin Awoyaya dake yankin Ibeju-Lekki.

Moses Oyekanmi ya ce cacar baki da cece-kuce ya barke a tsakanin likitan da kuma ma'aikaciyar lafiyar mai suna Dorcas Adeyara, wadda take aiki a asibitin likitan.

Al'amarin ya faru ne inda suka samu sabani akan yanayin dakin da wani mai jinya yake ciki, kuma hakan ta kai ga har ya mareta a fuska.

KU KARANTA: An kama wasu mutane 7 masu hannu a rikicin jihar Filato

"Mai girma mai shari'a wanda ake tuhuma ya yi mata rauni a dalilin marin da yayi mata, ya mareta ne saboda yana ganin tana aiki a karkashinsa, dan haka ya kamata a hukunta shi bisa wannan laifi da ya aikata", inji jami'in dan sandan.

Laifin ya saba da sashi na 172 na kudin laifuka na jihar Legas na shekara ta 2015. Aikata laifi irin wannan zai iya jawo wa mutum zama a gidan kaso har na tsawon shekaru 3.

Wanda ake zargin, ya musanta tuhumar da ake masa a gaban kotun, daga nan ne alkalin kotun O.A Fowowe-Erusiafe, ta bada belinsa akan kudi Naira dubu 50,000.

Alkalin kotun ta bada belin ne bisa sharadin samun wanda zasu tsaya masa sannan dole ne su zamo suna da shaidar biyan haraji har na tsawon shekaru biyu ga gwamnatin jihar Legas.

A karshe Fowowe-Erusiafe ta dage shari’ar har zuwa 19 ga watan Agusta domin sake cigaba da sauraron shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng