Babbar nadama ta rayuwa shi ne zama a Arsenal har na tsawon shekaru 22 - Wenger

Babbar nadama ta rayuwa shi ne zama a Arsenal har na tsawon shekaru 22 - Wenger

- Magoya bayan kungiyar Arsenal tabbas ba za su so jin fitar kalama irin wannan daga bakin tsohon kochin nasu ba

- Mai horas da kungiyar ya bayyana nadamar zamansa har na shekara sama da ashirin

- Kuma ya ce nan gaba zai sanar da makomarsa

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger, ya bayyana cewa zaman da ya yi a kungiyar kwallon ta Arsenal na tsawon shekaru 22 babban kuskure ne a rayuwar aikinsa na horas da ‘yan wasa.

Babbar nadama ta rayuwa shi ne zama a Arsenal har na tsawon shekaru 22 - Wenger
Babbar nadama ta rayuwa shi ne zama a Arsenal har na tsawon shekaru 22 - Wenger

Sannan ya ce yana da na sanin zaman da yayi tare da sadaukarwa akan aikin da na yi a kungiyar ta Arsenal.

Kocin dan asalin kasar faransa mai kimanin shekaru 68 a duniya, ya fara aiki da kungiyar ta Arsenal ne a cikin watan Oktobar 1966, ya bayyana hakan ne a cikin wata zantawa da akayi da shi a wata kafar yada labarai ta RTL.

KU KARANTA: Hukumar Hisbah ta yi ram da Almajirai 500 dake yawon bara a garin Kano

Kuma ya ce nan da wasu watanni kadan masu zuwa zai yanke shawarar makomarsa.

"Zaman da na yi na tsahon shekaru 22 a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ba karamin kuskure ba ne, kuma na yi nadamar hakan, saboda na fahimci na sabawa mutane da yawa a dalilin zaman da na yi. Ni mutum ne mai son sababbin abubuwa tare kuma da chanji, a daya bangaren kuma ina son a kalubalance ni"

"Amma sai ga a dalilin sadaukar da komai na da nayi ga kungiyar na yi nesa da makusanta na da ‘yan uwa da abokan arziki ciki har da iyalai na’’. In ji Wenger

Ya kara da cewa a dukkanin lokacin da kungiyar kwallon kafan ta Arsenal ta fito domin buga kwallo, to babban burina bai wuce ganin ta yi nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng