Yara yan arewa miliyan 12 basa makaranta – Inji Ango Abdullahi
Tsohon shugaban makarantar Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, Farfesa Abdullahi Ango a ranar Talata, 17 ga watan Yuli ya bayyana cewa imanin yara miliyan 12 basa makaranta a Najeriya, wanda mafi akasarisu yan arewacin kasar ne.
Abdullahi wanda ya bayyana hakan a wajen taron yaye dalibai da kuma cikar makarantar Zaria Academy shekaru 20 da kafuwa yace wannan adadi da ya fadi yana la’akari ne da rahoton kidaddiga.
Tsohon shugaban jami’ar ya bayyana cewa wannan lamari ya kasane barazana ga tattalin arziki da tsaron yankunan inda ya kara da cewa ya zama dole a inganta ilimi domin magance matsalolin da arewacin kasar ke ciki a yanzu.
KU KARANTA KUMA: Zaben Ekiti: Hukumar INEC ta bayar da takardan shaidar dawowa mulki ga Fayemi
Ya kalubalanci mutane masu kudi a arewa da su samar da makarantu sannan su dauki nauyin ilimin yara marasa karfi a garuruwansu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng