Tsiyar nasara sai za shi gida: Zamu baku mamaki r-APC ga APC

Tsiyar nasara sai za shi gida: Zamu baku mamaki r-APC ga APC

- Rikicin cikin gida tsakanin rAPC da APC na daukar sabon salo

- Inda yanzu haka rAPC ke yiwa APC Albishirin shan kayi a zaben 2019

- Wannan na zuwa ne bayan da a kwanakin baya APC ta ce 'yan rAPC tamkar 'yan cirani ne

A ranar Talata ne tsagin sabuwar jam’iyyar APC mai lakabin R-APC ya zargi jam’iyyar APC akan amfani da kudin harajin da aka tattara wajen siyan kuri'un masu kada zaben da aka yi a jihar Ekiti.

Tsiyar nasara sai za shi gida: Zamu baku mamaki r-APC ga APC
Tsiyar nasara sai za shi gida: Zamu baku mamaki r-APC ga APC

Cikin wanta hira da aka yi da shi da jaridar Daily Independent kakakin tsagin R-APC Yarima Kassim Afegbua, ya bayyana cewa tabbas jamiyyar APC za ta sha kasa a zaben 2019 da ke tafe.

Ya kara da cewa ‘’Lamarin siyasa ba lamari ne na surutu ko babatu ba, a'a siyasa tana bukatar tsari da jajircewa domin kaiwa ga nasara. Zancen da mu ke yanzu, kun san mun tafi gaban alkali, sannan kuma muna tattaunanawa tare da tuntuba domin cimma abin da mu ke bukata.’’

"Duk wanda ya ke zaton zamu dinga babatu ne ko ragaita akan hanya domin ajiyo amonmu, to babu shakka tunaninsa bai kai inda mu ka nufa ba".

Kassim ya kuma cigaba da cewa ‘’Zamu baiwa wadanda suke kallon babu wanda ya isa ya yi nasara akan shugaba Muhammad Buhari mamaki, domin kuwa wannan shi ne matakin farko da zai kai shugaban kasa Buhari zuwa ga rashin nasara’’.

KU KARANTA: Tabargaza: ‘Yan sanda sun rarumi wani likitan bogi bayan ya kashe mutum 2 da sunan tiyata

Ya ce da farko babu irin sunayen da ba'a kirawo mu da shi ba, amma sai ga shi ana binmu har gida ana bamu hakuri akan kar mu fice daga jamiyyar APC.

Da ya juyo batun zaben jihar Ekiti kuwa, ya bayyana matukar takaicinsa akan abin da ya faru. Inda ya ce "Jamiyyar da take furtar cewa tana yaki da cin hanci da rashawa, kuma wacce ta samar da gwamnati mai adalci dake yin abubuwanta a bude ba tare da wani nuku-nuku ba, amma sai ga shi ta murde sakamakon zaben jihar Ekiti ta hanyar magudin zabe tare da amfani da kudi" Kassim ya jaddada.

A karshe ya ce lokaci yana nan zuwa da yan kasar nan za su yi watsi da jamiyyar APC wacce zata gaza kai bantenta a kakar zaben shekarar 2019, wanda a lokacin babu jami'an ‘yan sanda 30,000 tare da jami'an soji 10,000 da za'a kai kowacce jiha a fadin kasar nan, kamar yadda aka kai jihar Ekiti.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel