Makiyaya sun damke barayin shanayensu yayinda suka kawo kasuwa sayarwa, sun kashe su nan take
- San banzar wasu barayin Shanu ya zama ajalinsu
- Bayan sun sace Shanunmakiyay ne kuma suka kai kasuwar Fulanin domin siyarwa, ashe sun gane kayansu
Makiyaya sun kashe wasu barayin shanu guda shida a yayin da suka kai shanu kasuwar Iware dake Ardo-kola a jihar Taraba domin sayarwa.
Rundunar yan sanda ta shaidawa manema labarai faruwar lamarin, inda suka ce barayin sun kai shanun kasuwar yankin Lai wanda a nan ake rikicin Fulani da Makiyaya domin su sayar da su, amma su kayi rashin sa'a Fulanin suka gane shanunsu, abinda ya kai ga har barayin sun rasa rayukansu.
KU KARANTA: ‘Yan sanda sun harbe wata mata yayin zanga-zangar da suke yi kan kashe abokan aikinsu 2 a Kaduna
Kakakin hukumar yan sanda ta jihar ASP David Misal, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Misal ya ce "Ya zuwa yanzu bamu samu cikakken bayani akan wadnda aka kashen ba, sannan ba zamu iya tabbatar ko daga yankin Lau suke ba".
"Muna cigaba da bincike domin gano wanda suka dauki doka a hannunsu maimakon su kawo wa hukuma domin yin bincike".
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng