‘Yan sanda sun harbe wata mata yayin zanga-zangar da suke yi kan kashe abokan aikinsu 2 a Kaduna

‘Yan sanda sun harbe wata mata yayin zanga-zangar da suke yi kan kashe abokan aikinsu 2 a Kaduna

- Bisa kuskure 'yan sanda sunyi sandiyyar ajalin wata mata

- Lamarin ya afku ne yayin da 'yan sandan suke zanga-zangar nuna alhinin mutuwar abokan aikinsu biyu

- A 'yan kwanakin nan dai jami'an 'yan sanda na cigaba da fuskantar barazanar hari daga 'yan ta'adda daban-daban

A jiya ne jami'an rundunar ‘yan sandan ta kasa reshen jihar Kaduna suka harbe wata mata a lokacin da su ke gudanar da zanga-zangar lumana bisa dalilin kashe abokan aikinsu su biyu da yan bindiga su ka yi a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

‘Yan sanda sun harbe wata mata yayin zanga-zangar da suke yi kan kashe abokan aikinsu 2 a Kaduna
‘Yan sanda sun harbe wata mata yayin zanga-zangar da suke yi kan kashe abokan aikinsu 2 a Kaduna

Matar ta hadu da ajalinta ne a lokacin da wani jami'in dan sanda ya harba bindigar da ke hannunusa sama yayin zanga-zangar domin nuna cewa lallai ransu ya baci.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa reshen jihar Kaduna ASP Mukhtar Hussain ya bayyana cewa a ranar litinin din da ta gabata ne su kayi artabu da wasu yan bindiga a lokacin da suke tsaka da sintiri a kauyen Tabani da ke kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.

KU KARANTA: Rashin nasarar PDP a kotu ya jawo zata biya N600,000 ga Ali Modu-Sheriff da wasu mutune biyu

“Mun yi musayar wuta da ‘yan bindigar a inda su ka harbi jami'an mu guda biyu, bayan garzayawa asibiti da su domin ceto lafiyarsu, amma rai yayi halinsa. Sannan suka kwato bindiga kirar AK 47 a gurin da lamarin ya faru" in ji ASP Mukhtar Hussaini.

A karshe ya yi Kira ga al'umma da su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba, domin an samu zaman lafiya a inda al'amarin ya faru

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel