Hauka-maganin ka Allah: Sabon addinin bautar Shugaba Trump ya bulla a kasar Indiya

Hauka-maganin ka Allah: Sabon addinin bautar Shugaba Trump ya bulla a kasar Indiya

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da bullar wani sabon addin a kasar Indiya inda ake bautawa hotunan shugaban kasar Amurka Donald Trump.

Kamar dai yadda muka samu, wani manomi a kasar mai shekaru 31 a duniya mai suna Bussa Krishna shine ya assassa addinin yake kuma ta yin abin sa kusan shekaru uku da suka gabata.

Hauka-maganin ka Allah: Sabon addinin bautar Shugaba Trump ya bulla a kasar Indiya

Hauka-maganin ka Allah: Sabon addinin bautar Shugaba Trump ya bulla a kasar Indiya

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya tayi asarar jami'ai 23

Legit.ng ta samu daga majiyar mu ta Oddity Central cewa shi dai Krishna dan asalin kauyen Konne ne dake a jihar Telengana kuma yana yin ibadar sa a gaban hoton Trump din sau da yawa a rana.

Sai dai kuma hakan ya sa jama'ar yankin ke yi masa kallon wani mai tabin hankali domin a nasu ra'ayin mahaukaci ne kawai zai iya yin hakan.

Da aka shawarce shi ma yaje yaga likitan mahaukata, Krishna ya bayyana cewa shi ba inda zai je don kuwa yana da hankalin sa garas kuma yace yayi amannar cewa Trump din zai iya taimakon sa idan har ya roke shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel