Kalli dalilan da suke sanya samarin mu shiga shaye - shaye

Kalli dalilan da suke sanya samarin mu shiga shaye - shaye

- Rashin bawa matasa aikin yi yana cefa wasu daga cikin su fadawa harkar shaye -shaye

- Yakamata gwamnati ta sanya Ido akan harkar shaye -shaye da sauran laifuffuka da ake aikatawa

Kalli dalilan da suke sanya samarin mu shiga shaye - shaye
Kalli dalilan da suke sanya samarin mu shiga shaye - shaye

Shugaban dake kula da hukumar harkar cigaban matasa na Nageriya (NYCN) Comrade Abdullahi Suleiman Ango yace matsalar shaye-shaye da ake fama da ita tana da nasaba da sakacin iyaye a ciki.

Ango wanda ya tattauna da manema labarai a ranar Juma'a a sakateriya dake Abuja yace matsalar shaye-shaye ta zama ruwan dare a ko ina a fadin kasar nan, yace iyaye, gwamnati da kuma gwamnatin tarayya basa kulawa da hakkokin dake kansu.

DUBA WANNAN: Wargi ma wuri yake samu: Kalli irin mutanen da hukumar EFCC ta kama a watanni shida

"Idan mukai duba da abinda ke faruwa a yanzu matasa sun zama karfen kafa ba akan harkar shaye -shaye kadai ba amma idan mukai duba da asalin abun zamuga cewa sakaci ne daga wajen iyaye".

Rashin aikin yi ya jefa wasu daga cikin matasan fadawa harkar shaye shaye da kuma fashi da makami.

Ango yace ya kamata gwamnati ta sa ido akan harkar shaye shaye sannan ta dunga tafiyar da kungiyoyin matasan da kuma aikin sa kai da sukeyi.

"Duk da cewa aikin gwamnati zaiyi wahalar samuwa amma matasan suna bukatar kulawa."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng