Dan da kyar: Komai ya kammala na bayar da belin Dasuki, har alkali ya rattaɓa hannu

Dan da kyar: Komai ya kammala na bayar da belin Dasuki, har alkali ya rattaɓa hannu

- Watakila iyalan Sambo Dasuki su zuba ruwa a kasa su sha don murna

- Bayan bayar da shi beli, yanzu haka ya cika duk sharuddan da alkali ya gindaya masa

- Tun farko dai gwamnatin tarayya ce ta cafke shi tun a shekara ta 2015

Tsohon mashawarci a harkokin tsaro na ƙasa lokacin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya na shirin shaƙar iskan sarari nan da kowanne lokaci sakamakon amincewa da bayar da shi beli da alkalin wata babbar kotu ya sake yi.

Dan da kyar: Komai ga kammala na bayar da belin Dasuki, har alkali ya rattaɓa hannu
Dan da kyar: Komai ga kammala na bayar da belin Dasuki, har alkali ya rattaɓa hannu

Alkalin mai suna Ijeoma Ojukwu ya dai amince da bayar da Dasukin beli ne tun a ranar 12 ga watan Yulin da muke ciki na 2018.

Dasuki dai ya kasance a tsare ne tun bayan da jami'an hukumar tsaron sirri suka sake damke shi a danar 29 ga watan Disambar shekarar ta 2015.

Mai shari'a Ojukwu ya amince da rattaɓa hannu kan takardar bayar da shi belin ne bayan ya cika duk sharuɗɗan da kotun ta gindaya masa.

Wata majiya daga dangin Dasukin ta bayyana cewa, ƴan uwansa ne da abokna arziƙi suka yi huɓɓasar cika ƙa'idojin dake ƙunshe cikin sharuɗɗan belin, kuna ma'aikatan kotun sun tantance ƙa'idojin da suka gabatar tun makon da ya gabata.

KU KARANTA: Kotu ta hana Dasuki bukatar da ya nema na a biya shi N5bn na barnar da aka yi masa

Rattaɓa hannu kan takardar belin na nufin za'a iya sakin Sambo Dasukin nan da kowanne loakci.

Rahotanni sun bayyana cewa iyalai da dangi har ma abokan arzki ne suke ta tururuwa zuwa Abuja don tarɓarsa idan an bi umarnin kotun na sakin shi.

Tun farko dai Dasukin ya shigar da buƙatar bayar da shi beli ne kasancewar an tsare shi tun shekara ta 2015 ba tare da yi masa shari'a ba, wanda hakan ya kasance tamkartauye masa hakinsa na ƴancin walwala ne a matsayinsa na bil Adam.

Dan da kyar: Komai ga kammala na bayar da belin Dasuki, har alkali ya rattaɓa hannu
Dan da kyar: Komai ga kammala na bayar da belin Dasuki, har alkali ya rattaɓa hannu

Bayan shafe shekaru biyu a tsare, kotun dai ta amince da karɓar ƙorafin nasa, kuma a bisa ƙorafin tauye masa haƙƙin ta bayar da shi belin a ranar 2ga watan Yuli 2018.

Duk da yake gwamnatin tarayya ce ke yin ƙarar tsohon mashawarcin a kotuna daban-daban har huɗu, an sha bayar da shi beli amma gwamnatin bata bin umarnin sakin nasa.

Har sai da ta kai kotun Afirka ta yamma ta umarci a bayar da shi beli da kuma biyansa N15m bisa tsare shi ba bisa ƙa'ida ba, amma gwamnatin Najeriyar ta yi kunnan uwar shegu da wancan umarni.

Daga yanzu dai ido za'a cigaba da zurawa don ganin ko gwamnatin zata bi umarnin kotu a wannan karon.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng