Sani Danja yayi murnar cika shekara 11 aurensa da Mansura Isa
Shahararren jarumin nan na masana'antar Kannywood kuma tauraro a masana'antar Nollywood, Sani Musa Danja yayi murnar cikarsa shekaru 11 da aure.
Jarumin ya raya ranar auren sa da matar sa kuma tsohuwar jarumar fina-finan hausa, Mansura Isa.
Ma'auratan sunyi murnar zagayowar wannan rana a kashen makon da ya shige.
Jarumin yayi murnar zagayowar wannan rana a shafin sa na kafar sada zumunta. Ya wallafa hoton shi tare da uwargidan tasa inda ya rubuta sako mai narkar da zuciya.
Allah ya azurta ma’auratan da haihuwar yara hudu, maza uku da mace guda.
KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Bamu kori Ortom daga jamiyyarmu a – APC ta maida martani
Mansura Isa tana daya daga cikin tsofafin jarumai yan fim da suka nishadantar da al'umma shekarun baya. tauraron ta ya haska matuka.
Sai dai bayan aurenta aka daina jin duriyar ta a farfajiyar fim.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng