Yanzu Yanzu: Sanatan Adamawa da wani dan majalisa 1 sun bar APC, sun koma ADC

Yanzu Yanzu: Sanatan Adamawa da wani dan majalisa 1 sun bar APC, sun koma ADC

Sanata Abdul-Azeez Nyako dake wakiltan Adamawa ta tsakiya da Rufai Umar mai wakiltan mazabar Gombi a majalisar dokokin Adamawa sun sanar da sauya shekarsu daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Da suke sanar da sauya shekarsu a ranar Litinin a taron masu ruwa da tsaki da kaddamar da kwamitin ADC na Adamawa a Yola, yan majalisan sun bayyana cewa sun bar APC tare da magoya bayansu saboda rashin adalcin da aka yi masu a taron APC a Adamawa kwannan nan.

“Muna fata tare da addu’an Allah ya sa matakin da muka auka ya zamo mafi ahla a gare mu.

Yanzu Yanzu: Sanatan Adamawa da wani dan majalisa 1 sun bar APC, sun koma ADC

Yanzu Yanzu: Sanatan Adamawa da wani dan majalisa 1 sun bar APC, sun koma ADC

“Adalci shine ginshikin ko wani kyakyawan abu sannan muna son jan hankalin ADC da ta tabbatar da adalci domin a samu Karin mutane da yawa.” Inji Abdul-Azeez.

A halin da ake ciki, Jam’iyyar Progressives Congress APC ta maida martani ga rahoton cewa gwamnan jihar Benue, Dr Samuel Ortom ya bar jam’iyyar, cewa bata samu labarin hakan kai tsaye daga gare shi ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Babban hadimin Dogara ya bar APC

Da yake Magana a ranar Litinin, a Abuja jim kadan bayan taron kwamitin aiki na jam’iyyar, shugaban APC, Kwamrad Adams Oshiomhole yace gwamnan yayi alkawari lokuta da dama kan cewa ba zai bar jam’iyyar ba sai dai idan an kore shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel