Yan kwallon kasar Faransa Musulmai 7 da suka taimaka wajen daga kofin duniya
Yayinda kasar Faransa ta lallasa kasar Kroshia a wasan karshen na gasar kwallon kafar duniya da kaayi a Rasha, Legit.ng ta kawo muku jerin yan kwallon kasar Faransa Musulmai bakwai da suka bada gudunmuwa wajen samun wannan nasara.
1. Paul Pogba
Asalinsa dan kasar Guinea ne, ya kasance yana bugawa kungiyar kwallon Jubentus kafin ya koma Manchester United. Shine yaci kwallo na 3 a wasar karshe.
2. Ousmane Dembele
Dan shekara 21 kacal wanda yake da asali daga kasar Mali, Mauritania ko Senegal. Yana bugaba kungiyar kwallon kafar Barcelona.
3. N’Golo Kante
Jarumin dan kwallo wanda asalin dan kasar Mali ne. shine ya taimakawa kungiyar kwallon Leicter City wajen daga kofin Ingila a 2015. A yanzu haka yana bugawa Chelsea.
4. Adil Rami
Balarabe kuma dan asalin dan kasar Maroko ne wanda ya koma kasar Faransa da kwallo.
5. Djibril Sidibe
Asalin dan kasar Senegal kuma dan shekara 24 wanda ya zama dan kasar Faransa.
6 Benjamin Mendy
Shima dai asalinsa daga kasar Senegal ne. yana bugawa kungiya kwallon kafar Manchester City.
7. Nabil Fekir
Balarabe kuma dan asalin kasar Algeria. Ya taka rawar gani a wasan karshen bayan ya canji lamba 9, Giroud.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng