Kwamitin mutum 11 zai soma bincikar Obasanjo da Jonathan kan badakalar satar kudi
Mambobin majalisar wakillan tarayyar Najeriya sun shirya tsaf da nufin fara yiwa tsaffin shugabannin Najeriya Cif Obasanjo da kuma Jonathan binciken kwa-kwaf game da kudaden da ake zargin an sake sacewa bayan an kwato su daga hannun iyalan Abacha a lokacin su.
Majalisar dai ta nada kwamitin mutane 11 ne karkashin jagorancin Honorable Abdulmumini Jibrin kuma kamar yadda muka samu, za su soma aikin su ne a cikin satin nan mai kamawa.
KU KARANTA: Jerin shugabannin kasashe 10 masu karfin arziki
Legit.ng ta samu cewa sai dai a wani mataki da ake ganin kamar na nemar wa shugabannin sauki ne, shugaban kwamitin ne ya dauri niyyar zuwa har gidan tsaffin shugabannin kasashen domin yayi masu tambayoyi kan batun.
Sauran wadanda kwamitin zai bincika dai sun hada da babbar ministar harkokin kudi Kemi Adeosun, Antoni Janar na kasa Abubakar Malami, Shugaban babban bankin tarayya Mista Godwin Emefiele da kuma tsohuwar ministar kudi Dakta Ngozi Okonjo Iweala.
Haka ma kwamitin zai gayyaci tsaffin Ministocin Shari'a da na kudi da kuma shugabannin bankin tarayya a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa marigayi Ummaru Musa Yar'adua.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng