Masarautar Saudiyya ta garkame babban malamin sunna Sheikh Safar al Hawali

Masarautar Saudiyya ta garkame babban malamin sunna Sheikh Safar al Hawali

Masarautar daular Saudiyya ta kama tare da kulle daya daga cikin manyan malaman sunna kuma marubuci a daular mai suna sheikh Safar al Hawali a kan wani littafin da ya wallafa a 'yan kwanakin nan.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, babban malamin ya soki yadda wasu daga cikin 'ya 'yan masarautar ke gudanar da rayuwar su a cikin wani sabon littafinsa da ya wallafa.

Masarautar Saudiyya ta garkame babban malamin sunna Sheikh Safar al Hawali

Masarautar Saudiyya ta garkame babban malamin sunna Sheikh Safar al Hawali

KU KARANTA: An kama dan majalisa a Najeriya da bindigogi

Legit.ng ta samu haka zalika cewa a kwanan bayan an taba kama malamin tare da kulle shi saboda ya soki yarjejeniyar da daular ta shiga da sojojin Amurka.

Sai dai tuni 'yan kungiyoyin sa kai masu fafutuka sun soki kasar ta Saudiyya da musamman ma ganin yadda take ta kara dabbaka wasu shire shiren da suka sabawa shari'ar Musulunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel