Ba lafiya: Sojoji da 'yan kato-da-gora da dama sun bace bayan samamen 'yan ta'addan Boko Haram

Ba lafiya: Sojoji da 'yan kato-da-gora da dama sun bace bayan samamen 'yan ta'addan Boko Haram

Wasu jami'an sojin Najeriya tare da kwamandan su hadi da wasu 'yan kato-da-gora da dama a garin Bama na jihar Borno an ruwaito cewa sun bace biyo bayan wani samame da ake kyautata zaton 'yan ta'addan Boko Haram ne suka kai masu.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, wadanda suka bace din da a halin yanzu tuni aka kaddamar da shirin nemo su, sun bace ne bayan samamen da aka kai masu ranar Juma'ar da ta gabata.

Ba lafiya: Sojoji da 'yan kato-da-gora da dama sun bace bayan samamen 'yan ta'addan Boko Haram

Ba lafiya: Sojoji da 'yan kato-da-gora da dama sun bace bayan samamen 'yan ta'addan Boko Haram

KU KARANTA: PDP aljanna ce a siyasar 'yan Najeriya - Ambasada Kazaure

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas sun sanar da samun nasarar cafke dan majalisa a jihar mai suna Dipo Olorunrinu da laifin mallakar wasu haramtattun bindigu da alburusai ba bisa ka'ida ba.

Shi dai dan majalisar an kama shi ne biyi bayan wasu mutane da yan sandan suka kama da bindigu suka kuma ayyana shi a matsayin wanda ya basu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel