Abin mamaki: Bayan shekaru 20 da aure tsohuwa mai shekaru 52 ta haifi santaleliyar ‘yarta (Hotuna)
- Murna baki har kunne ga wata mai jego tsohuwa bayan dadewa bata haihu ba
- Haifo santaleliyar 'yarta ta ya sanya mutane da dama ban mamaki kasancewar tsufa ya fara jimmata
A duk lokacin da aka samu haihuwa iyalan da su ka samu wannan karuwar su kan kasance cikin farin ciki marar misaltuwa, musamman idan aka yanke tsammanin haihuwa daga wacce tayi haihuwar sabo da shekarun da ta dauka ba tare da haihuwar ba.
Wannan al'amarin ne ya faru a cikin zuri'ar Ogundero Dainty Morenike da ke jihar Ekiti a lokacin da wata gwaggonsu mai shekaru 53 da haihuwa a duniya ta haifi zankadediyar ‘yar ta mace.
KU KARANTA: Asirin wata budurwa da ta saci jaririn sati 3 da haihuwa ya tonu, duba hoton
Tun da farko dai ta sanar da labarin haihuwarta ta ne a shafin ta na facebook, in da ta ce bayan shekaru 20 da yin aurensu, sai yanzu Allah ya ba ta rabon haihuwar 'ya mace wacce ta sanya mata suna Victoria.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng