EFCC ta karyata zargin Magu da cinye kudin alawus din ma'aikata

EFCC ta karyata zargin Magu da cinye kudin alawus din ma'aikata

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta musanta wani rahoto da ya zargi shugabanta, Ibrahim Magu, da karkatar da miliyan N702 daga albashin ma'aikata na watanni 13.

Ana zargin EFCC ne da gaza biyan kudin alawus da albashi na wasu jami'anta da suka karbar wani horo a makarantar horon sojoji ta NDA.

Da yake mayar da martani a kan zargin da ake yiwa EFCC, kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, ya karyata zargin cewar akwai wasu ma'aikata da ba a biya su albashi ko wasu alawus ba.

EFCC ta karyata zargin Magu da cinye kudin alawus din ma'aikata
EFCC ta karyata zargin Magu da cinye kudin alawus din ma'aikata

DUBA WANNAN: Jerin mutanen da PDP ta fitar da zasu gana da Obasanjo da kuma dalilin ganawar su

Uwujaren ya bayyana cewar wasu marasa kishin kasa ne da basa jin dadin aiyukan da hukumar ke yi suka kirkiri wannan karya domin kawo rudani da raini tsakanin sabbin ma'aikata da shugabancin hukumar EFCC.

Kazalika ya sanar da cewar EFCC ta biya dukkan jami'anta kudin alawus na kwas din da aka tura su tun ranar 11 ga watan Mayu. Saidai ya bayyana cewar babu alawus ga wasu ma'aikata da aka tura kwas din kwanaki 28, kamar yadda yake cikin kundin tsarin EFCC.

Uwujaren ya ce tabbas akwai wasu ma'aikatan da basu samu albashinsu na watan Yuni ba, amma hakan ya biyo bayan rashin kasancewar su a sabon tsarin nan na gwamnatin tarayya dake tattara bayanan dukkan ma'aikatanta wato IPPS.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: